Featured
Tinubu ya ɗage taron majalisar zartaswa sakamakon mutuwar Lagbaja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin dage taron majalisar zartaswa zuwa wani lokacin sakamakon mutuwar babban hafsan sojan kasa Taoreed Lagbaja.
Tun farko dai an shirya gudanar da taron ne yau Laraba, amma shugaban ya bayar da umarnin dage shi domin girmama babban hafsan sojin wanda ya rasu a daren Talatar makon nan.
Marigayi Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya rike mukamin babban hafsan soji daga ranar 19 ga watan Yunin 2023, har zuwa rasuwarsa 5 ga watan Nuwamban bana.
A jawabinsa, shugaba Tinubu ya ba da umarnin yin kasa-kasa da Tutoci na tsawon kwanaki bakwai.
Da safiyar yau Laraba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayi Lagbaja da rundunar sojin Najeriya.