Featured
Akwai matsala idan Tinubu yayi amfani da ƙarfin ikon sa wajen ganin kudirin gyaran haraji ya wuce – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya ce, bai kamata a aiwatar da dokar garambawul ta haraji da Shugaba Tinubu yakeso ayi a yadda take ba.
Gwamna Zulum, ya kara da cewa idan har aka amince da kudirin, mafi yawan kudaden da ake samu daga harajin na (VAT) za su je jihar Legas ne.
Sai dai ya yi gargadin cewa, idan har Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi amfani da karfinsa wajen ganin an zartar da kudirin a gaban majalisar dokokin kasar nan ba tare da yin gyare-gyaren da ya kamata ba, to al’ummar Najeriya bazasu ji dadi ba
Zulum, ya tabbatar da cewa shi ba ya adawa da gwamnatin Shugaba Tinubu, amma ya nemi karin lokaci domin tuntubar juna kan shawarwarin sake fasalin harajin bisa tsarin dimokuradiyya.
“Mun san karfin ikon da Shugaban kasa yake da shi, ina girmama shi, idan Shugaban Kasa yana so yayi amfani da karfin sa wajen ganin wannan kudirin gyaran harajin ya wuce tabbas zai iya, amma kudirin bazai yi wa yan kasa dadi ba”. Gwamnan na Borno ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar channels a ranar Lahadi 01, ga Disamba 2024.
Duk da adawar da wasu ɓangarorin suka yi akan kudurin, Majalisar Dattawa ta mika kudorin don karantu na biyu.