Featured
Fiye da yara miliyan 10 aka yiwa rijistar haihuwa a Najeriya a cikin watanni uku – NPC.

Hukumar kula da yawan jama’a ta Najeriya (NPC), ta sanar da yiwa yara fiye da miliyan 10 rijistar haihuwa cikin watanni 3 da suka gabata.
Shugaban hukumar ta NPC, Alhaji Nasir Isa Kwara, ne ya sanar da wadannan alkaluma, yayin zantawar sa da manema labarai, bayan ziyarar da mai ɗakin Shugaban Ƙasa Sanata Oluremi Tinubu ta kai, tare da karrama jaririn farko da aka haifa cikin shekarar nan ta 2025, a Asibitin Asokoro da ke Abuja.
Shugaban wanda ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka na hukumar Bala Banya, ya bayyana cewa NPC na aiki tuƙuru wajen ganin kowanne jariri ya samu rijistar haihuwa da zarar an haife shi a ko’ina ya ke a sassan kasar nan.
Bala Banya ya kara da cewa, shirin rijistar jarirai sabbin haihuwa ya sake samun karɓuwa ne bayan haɗin gwaiwar da hukumar ta yi da asibitocin kula da lafiya a matakin farko, baya ga sabunta tsarin rijistar zuwa na zamani saɓanin yadda ya ke a baya.
A cewar sa, an yi wa yara fiye da miliyan 10 rijista cikin watanni 3 da suka gabata, wadanda suka ƙunshi sabbin haihuwa da kuma ƙananun yara ƴan ƙasa da shekaru 5 waɗanda ba a yiwa rijista a lokacin haihuwarsu ba.
Sai dai jami’in na NPC ya bayyana cewa, a yanzu sun fi mayar da hankali kan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 da ba a samu damar yi musu rijista ba.