Connect with us

Featured

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kudurorin Sauya Fasalin Dokar Haraji

Majalisar Wakilan ta Kasa ta amince da kudirin sake fasalin harajin da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar dokokin kasar.

A ranar Alhamis din nan ne Majalisar Wakilan ta amince da rahotan ƙudurorin gyaran harajin guda hudu a zaman da ta yi a Abuja, kamar yadda mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman kan yada Labarai ya wallafa a shafinsa na X.

A yanzu ana jiran amincewar Majalisar Dattijai ne.

Makasudin Ganawar Jakadan Najeriya A Nijar Da Ministan Harkokin Wajen Nijar

Kudurorin sun hada da dokar harajin Nijeriya da daftarin kula da haraji da dokar hukumar haraji, da kuma dokar kafa hukumar tattara kudaden shiga ta Nijeriya.

Wannan ya biyo bayan nazarin saɗara-saɗara na duk gyare-gyaren da suka dace akan kudurorin a Kwamitin Gabaɗaya.

Wasu daga cikin gyare-gyaren sun haɗa da barin harajin VAT a kan yadda yake a yanzu wato kashi 7.5 cikin 100, sabanin yadda aka so ƙara shi, da kuma tsawaita keɓance harajin kuɗin shiga ga takamaiman kasuwancin noma da jami’an soja.

Tare da amincewa da rahoton kan kudurorin haraji, Majalisar Wakilai na kokarin ganin ta amince da kudirin haraji a mako mai zuwa yadda zai zama doka.

Tsarin raba kuɗaɗen haraji na VAT da majalisar ta amince da shi:

Za a dinga raba kashi 50 cikin 100 daidai wa daida ga jihohin ƙasar

Sai kuma a raba kashi 20 cikin 100 bisa ga yawan jama’ar jihohi

Kashi 30 cikin 100 kuma za a raba shi bisa ga abin da yawan abin da jihohin ke samarwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet