Featured
Duk Da Biyan Kudin Fansa, ‘Yan Bindigar Basu Sako Janar Tsiga Ba

Tsahon kwanaki 40 ke nan bayan garkuwa da tsohon shugaban Hukumar Kula da Masu Yiwa Ƙasa Hidima ta Kasa Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da ƴanbindiga suka yi, har yanzu basu sako shi ba duk da cewa an biya kuɗin fansa.
Rahotanni sun nuna cewar an biya maƙudan kuɗaɗe don ganin an sako Janar Tsiga, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 5 ga watan daya gabata.
Wata majiya ta kusa da iyalansa ta ce bayan kai kuɗin, sai da aka shafe mako guda kafin ƴanbindigar su sake tuntuɓar iyalansa, inda suka haɗasu ta waya, sannan kuma suka sake neman ƙarin wasu kuɗaɗe.
Da farko dai waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Janar ɗin, sun buƙaci a basu naira miliyan ɗari biyu da 50 a matsayin kuɗin fansa, sai dai an ci gaba da tattaunawa da su.
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF da kuma ta Dattijan Jihar Katsina KEF, sun buƙaci gwamnati da kuma rundunar sojojin ƙasar, su matsa kaimi wajen ganin an kuɓutar da shi da sauran mutanen da aka yi garkuwa tare da su.