Connect with us

Featured

Majalisar Dattawa Ta Dage Amincewa Da Kudirin Dokar Ta-ɓaci A Jihar Rivers

Majalisar dattawa a ranar Larabar nan ta samu rabuwar kawuna kan zartar da kudirin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas har zuwa ranar da za ta fara aiki.

Tun da farko dai majalisar ta dage tattaunawa kan kudurin wanda shine batu na farko a yau har zuwa karfe 3 na rana, ba tare da bayar da cikakken bayani kan jinkirin ba.

Ana sa ran za a yi muhawara tare da kada kuri’a a kan kudirin da shugaban majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya dauki nauyi a zaman da aka yi da safe. Sai dai ba zato ba tsammani, ‘yan majalisar sun jinkirta tattaunawar.

Kudirin ya nuna damuwa a fili kan yadda tashe-tashen hankula ke kara kamari, wanda ya durkusar da jihar tare da kawo cikas harkokin dimokuradiyyar mazauna cikinta.

“An damu da cewa akwai hatsarin gaske a halin yanzu na rikice-rikicen yayin da wasu bata gari ke barazanar yin kone-kone don kawo cikas ga harkokin tsaro.

“Ina da tabbacin cewa akwai bukatar samar da isassun matakai na yau da kullun don dawo da kyakkyawan shugabanci, zaman lafiya, doka oda da tsaro a jihar Ribas”.

Don amincewa da sanarwar, Majalisar Dattawa na buƙatar rinjaye kashi biyu bisa uku (73 daga cikin 109) don ba da damar dokar ta-baci ta fara aiki.

A ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers bayan da aka dade ana fama da rikicin siyasa a jihar Kudu maso Kudu mai arzikin man fetur.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi da ya yi a fadin kasar, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara; mataimakinsa Ngozi Odu; da dukkan ‘yan majalisar na tsawon watanni shida.

Shugaban kasar ya zabi Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin mai kula da harkokin jihar na tsawon watanni shida na farko.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet