Connect with us

Featured

Dakarun Sojojin Sudan Sun Sake Ƙwace Ikon Fadar Shugaban Ƙasa

Dakarun rundunar Sojojin Sudan sun sake ƙwace fadar shugaban ƙasar daga hannun dakarun sa-kai a yau Juma’a bayan da aka gwabza kazamin fada, kamar yadda wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

“Dakarun mu sun kai farmaki fadar shugaban ƙasa inda suka mamaye ta bayan murkushe ragowar ‘yan tawayen RSF,” in ji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.

Tana magana ne ga Rundunar Rapid Support Forces (RSF), ‘yan tawayen da suka mamaye kujerar shugaban kasa a Khartoum tun bayan barkewar yaki da sojoji a watan Afrilun 2023.

A farkon makon nan ne dai rundunar sojin ƙasar ta Sudan tare da hadin gwuiwar wasu dakarun suka fatataki yan tawayen RSF a wannan yaki a tsakiyar birnin Khartoum.

Kusan shekaru biyu kenan da ake gwabza yaki tsakanin hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhane da tsohon mataimakinsa kuma kwamandan RSF Mohamed Hamdane Daglo.

Rikicin dai ya yi sanadin mutuwar dubun dubatan mutane, tare da raba sama da mutane miliyan 12 da gidajensu, tare da janyo matsalar abinci da matsuguni mafi girma a duniya.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutane miliyan 3.5 a babban birnin Khartoum ne aka tilastawa barin gidajensu sakamakon tashin hankalin, yayin da akalla mutane 100,000 ke fuskantar yunwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet