Connect with us

Featured

Majalisar Wakilai Ta Musanta Karɓar Kuɗi Don Amincewa Da Dokar Ta-ɓacin A Rivers

Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na cewa ta karɓi cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Honarabul Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa yawancin mambobin majalisar sun goyi bayan matakin ne domin kare dimokuraɗiyya da kuma tsare muradun al’ummar Jihar Ribas.

“Mun yanke shawarar ne bisa kishin ƙasa, haɗin kan siyasa, zaman lafiya, da kare dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Ya ce ya yi mamakin yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke baza jita-jita cewa an tilasta musu su amince da dokar ta-ɓaci tare da karɓar daloli.

A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa ’yan majalisa suna aiki ne don ganin an samar da tawagar sulhu kafin wa’adin dokar ta-ɓacin ta ƙare.

Ya jaddada cewa dole ne a kare dimokuraɗiyya a Najeriya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet