Connect with us

Featured

Majalisa Ta Bukaci A Rage Kudin Data Don Saukakawa Al’ummar Kasa

Majalisar Dattawan Kasar nan, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya.

A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong na Kuros Riba, ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200.

Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet.

“Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in ji Sanata Ekpenyong.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada cewa samun Intanet mai arha zai taimaka wa ƙananan ’yan kasuwa da tattalin arziƙin ƙasa gaba ɗaya.

Majalisar ta buƙaci gwamnati da ta tsara manufofi da za su tabbatar da farashi mai sauƙi, tare da kafa cibiyoyin fasaha masu rangwame ga ɗalibai, ’yan kasuwa, da masu aiki da fasahar zamani.

Haka kuma, ta umarci Kwamitin Sadarwa na majalisa da ya binciki dalilan tashin farashin data tare da nemo mafita mai ɗorewa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet