Featured
Majalisar Dokokin Kasar Nan Ta Nufi Hanyar Janye Rigar Kariya Ga Gwamnoni

Gwamnatocin Jihohin Kasar nan sun bayyana adamuwarsu da kudirin dokar da Majalisar Wakilai ta gabatar na neman a cire kariyar da tsarin mulki ya bai wa gwamnoni da mataimakansu da kuma mataimakin shugaban ƙasa daga fuskantar tuhuma kan laifuka.
Kudirin wanda ya tsallake karatu na biyu, na da nufin gyara sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, tare da jaddada kariya ga shugaban ƙasa kadai, wajen cire shi daga sauran manyan jami’an zartarwa.
A ranar Larabar da ta gabata ne ƙudirin ya samu karatu na biyu a zauren majalisar, ƙarkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.
Da wannan mataki, kai tsaye za’a mika shi ga kwamitin majalisar kan duba kundin tsarin mulki don ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen.
Yaƙi da cin hanci da rashawa
Masu goyon bayan kudirin, ciki har da wanda ya dauki nauyin gabatar da shi, Solomon Bob, sun yi zargin cewa cire rigar-kariyar zai ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma samun shugabanci na gari.
Sai dai kuma jami’ai a jihohi da masana harkokin shari’a sun yi gargadin cewa irin wannan matakin na iya kawo cikas ga gudanar da mulki, ta hanyar shari’u masu nasaba da siyasa, da ruguza sha’anin mulki, da rashin zaman lafiya a cikin gwamnatocin jihohi.
Matakin kariya da ke kunshe a sashe na 308 na ƙundin tsarin mulkin Najeriya ya kare shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu daga tuhuma a lokacin da suke kan karagar mulki.
An dai yi tanadin ne domin hana tarzoma da kuma tabbatar da cewa zababbun shugabanni sun mayar da hankali wajen gudanar da mulki ba tare da barazanar shari’a ba.
Sai dai kuma gyaran da ake shirin yi na neman shugaban ƙasa ne kawai zai mori wannan rigar kariya, tare da bai wa mataimakan shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu damar fuskantar shari’a kan zargin rashin da’a yayin da suke kan mulki.