Addini
Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Fara Duban Jinjirin watan Shawwal

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025.
Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakoto, Wazirin Sakoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi.
Wazirin Sakoto, ya yi addu’a Allah Ya taimaka musu a wannan muhimmin aikin na addini da suke yi.
Idan aka dace da ganin watan Shawwala a ranar Asabar, hakan na nufin za a yi sallah ƙarama a ranar Lahadi, akasin haka kuma za a yi sallah a ranar Litinin.
Yanzu haka dai al’ummar Musulmi sun mayar da hankali wajen shirye-shiryen bikin sallah ƙarama na bana.