Featured
Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Musanta Labarin Kona Mota Dauke Da ‘Yan Kabilar Igbo

Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kai hari ga wata mota mai dauke da fasinjoji ‘yan kabilar Igbo a Kano.
A cewar rundunar, wannan labari ba gaskiya ba ne, kuma ana neman hana yada irin wadannan rahotanni marasa tushe.
Kakakin rundunar yansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta zo ne kwana kadan bayan harin da aka kai wa wasu matafiya ‘yan Arewa a Uromi, Jihar Edo, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16.
Rundunar ‘yan sandan ta ce zuwa yanzu ta kama mutane 14 da ake zargi da hannu a wannan lamari, kuma ana ci gaba da bincike.
Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su guji yaɗa labaran karya, masu haddasa firgici da rura rikici a cikin al’umma.