Connect with us

Featured

Da Alama Zamani Ya Tafi Da Tuwon Sallah, Wanda Ke Neman Zama Tarihi

 

Saɓanin shekarun baya, lokacin da matan gida kan shafe tsawon wunin jajibere da daren sallah, suna haƙilon shirya tuwon sallah, a zamanin yau, kuna iya cin girkin sallah, ba tare da hayaƙi ko ƙauri sun bulbule ku ba.

Kwance cikin falon gida, babu kwaramniya da yarfe gumi a ɗakin girki, kuna iya buɗe kwano kawai, ku ci tuwon sallah mai daɗin gaske cikin annushuwa.

“Da sallah, akwai manyan mutane da manyan mata, saboda ba sa son wahala, za su zo, su ce a yi musu abincin sallah. Kuma idan an yi musu, za mu ɗauka mu kai musu har gida”, in ji wani mai gidan abinci da ake kira Shawarma House a Kano.

Ya ce abokan hulɗa kan zo tun sallah saura mako biyu, su ce a yi musu girkin shinkafa nau’i uku ko huɗu da dahuwar kaza nau’i biyu. Idan sun gama, sai su zuba a mazubai su kai wa mutum har gida.

Ba kawai daɗi da ƙamshin tuwon sallah ne ke da jan hankali ba a yanzu, yadda za a tsara zubin abincin a kwano ma abin la’akari ne

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan ƙayatarwa game da Sallar Idi tsawon zamani a ƙasar Hausa, shi ne tuwon sallah.

Abincin biki ne na musamman don ranar Idi, a birni da ƙauye, gidan talaka, da na mai kuɗi, har ma da masu mulki.

Alama ce ta al’ada da ke sanya annuri da annushuwa, gami da farin ciki a fuskoki.

Mai yiwuwa ma, yana cikin dalilan da suka sa, Sallar Idi ta zama bikin al’umma na shekara-shekara mafi burgewa, wanda Hausawa ke matuƙar ji da shi. Wata masaniya, Dr. Hadiza Salihu Koko ta ce asalin tuwon sallah, ba ya rasa nasaba da murna. An kammala azumin Ramadan lafiya.

“Ranar sallah, da ma ana so a kyautata, a inganta abinci, a lilwanta iyalai” in ji malamar, wadda ke koyarwa a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari a jihar Sakkwato.

Bayan shafe tsawon wata, ana ƙauracewa abin ci a wuni, yanzu lokaci ne na yin ban kwana da Ramadan mai alfarma. Ana kuma yin hakan ne, ta hanyar kyautatawa da yalwata alheri, da ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ‘yan’uwa da dangi, maƙwabta, kai har ma da baƙi.

Ƙaramar sallah tana buɗe ƙofar marmarin abincin da aka daɗe ba a ci ba, in ji wata matashiyar matar aure a birnin Abuja.

“Tun lokacin da aka fara azumi na ce ba zan ci tuwo ba. An fi cin abincin maƙulashe da tanɗe-tanɗe”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet