Featured
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 21 Da Aka Sace A Jihar Taraba

Rundunar yan sandan Kasar nan ta ce ta ceto mutum 21 da aka yi garkuwa da su a jihar Taraba da kuma ƙwace tarin makamai a wasu jerin samame da ta kai watanni uku na farkon wannan shekara ta 2025.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Olomuyiwa Adejobi ya fitar ranar Litinin, ya ce yawancin waɗannan samame an kai su a jihar Taraba ranar 29 ga watan Maris, kan hanyar Takum zuwa Mararaba.
Olomuyiwa ya ce an samu nasarar ƙwao mutanen ne bayan kazamin artabu a garin Muji da ke karamar hukumar Takum.
“Jami’an mu sun ɗauki tsawon lokaci suna artabu da masu garkuwan, kafin su samu nasarar kuɓuto da mutanen 20 tare da ababen hawa da suka tsere suka bari. Biyu daga cikin mutanen da suka raunuka da samun kulawa a asibiti,” in ji Olomuyiwa.
A ɗaya gefen, mai magana da yawun rundunar ta ƴansandan Najeriya ya ce jami’ai na musamman sun kama wani mutum bisa zargin fashi da makami da yin garkuwa da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
“Mun ƙwato bindigar AK49 da kuma harsasai yayin kamen. Ana ci gaba da bincike domin kama sauran mutanen da yake aikata ta’asar da su,” in ji sanarwar.