Connect with us

Featured

Kisan ‘Yan Arewa A Edo: Guda Cikin Mafarautan Da Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Ya Bayyana Yadda Ya Tsira

Abubakar Shehu, ɗaya ne daga cikin mafarautan da suka kuɓuta a harin, ya kuma bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya daga harin masu ɗaukar doka a hannun.

Ya ce wannan ne karonsa na farko da ya je farauta a Fatakwal, kuma a lokacin da suka isa Uromi, ƴan sintiri sun tare su.

“A lokacin da muka isa Uromi, sun tare mu a kan titi, suka ce mu sauko daga cikin mota.”

“Yayin da muka sauko sai suka fara dukanmu ba tare da sun tambaye mu komai ba.”

Da ya ga yanayin zai ɓaci, sai ya gudu ya ɓuya.

“Da suka fara dukanmu, wasu mutanen da ke wurin sun ce mana mu gudu.”

“A lokacin da na yi yunƙurin gudu, biyu daga cikinsu sun yi ƙoƙarin dakatar da ni, amma Allah ya ba ni sa’a ba su kamani ba.”

“Na ɓuya a wani kango, daga nan na riƙa jin duk abin da ya faru da ƴan’uwana.”

Daga baya cikin dare, kusan ƙarfe 10:00 na dare ya samu wani direban tankar mai ya taimake shi ya kai shi Kabo, daga nan ya iso Kano.

Shehu ya ce tun kafin ya tsira abokinsa Abdulkadir Umar, ya riga ya jikkata a hannun ƴan sintirin.

“Tun kafin na gudu, tuni Abdulkadir ya faɗi a ƙasa, abokaina sun samu munanan raunuka.”

Ya ce ƴan sinitirin ba su tambaye su, ko su wane ne su ba, kawai sun far musu ne.

“Muna da katunan shaidarmu da ke nuna cewa mu mafarauta ne, amma ba su tambaye mu komai ba.”

“Kuɗin da suka gani a hannunmu na mafarautan da ba su samu damar aika kudi gida ba ne.”

“Bindigogi da karnukan da muke tafiya da su, duka suna da takardun lasisi. Mu mafarauta ne ba ƴan fashin ba.”

Ya ce bai taɓa tsammanin zai rayu ba.

“Na yi tunanin cewa tawa ta ƙare, amma da ikon Allah na kuɓuta,” in ji shi.

Wasu daga cikin mafarautan Torankawa da aka kashe a Uromi

“Ƴaƴanmu ba masu laifi ba ne. Su ba ɓarayi ba ne, su mafarauta ne da ke fafutikar neman na kansu”, a cewar Sadiya Sa’adu mahaifiyar Haruna Hamidan, ɗaya daga cikin matasan da ƴan sintiri suka kashe a garin Uromi.

Kisan gillar da aka yi wa matasan wanda aka ɗauka a bidiyo sannan kuma aka yaɗa shi a shafukan sada zumunta, ya haifar da zazzafar muhawara da suka daga masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar.

A ranar Alhamis 27 ga watan Maris ɗin 2025 ne, aka kashe mafarautan a lokacin da suke kan hanyar su ta komawa Kano daga Farautar da suka je jihar Rivers.

Sadiya ta ce ɗan nata shi ke ɗaukar ɗawainiyar gidansu tun bayan rasuwar mahaifinsa.

“Shi ke ɗaukar ɗawainiyata da ta ƙannensa, don haka yanzu ba mu san yadda rayuwa za ta kasance da mu ba .”

Sadiya ta ce magana ta ƙarshe da ta yi da ɗan nata, ita ce kwana hudu kafin kisan, lokacin da ya aika mata da kuɗi domin sayayyar kayan sallah ga ƙaramin ɗansa.

“Na yi magana ta ƙarshe da shi ranar 22 ga watan Maris, lokacin da ta aiko mana da kuɗi domin sayen kayan sallah ga ƙaramin ɗansa, har ma na ce masa kuɗin ba za su isa ba, ya kuma ce zai yiwo ciko. Ya ma fa ce min ba zai zo gida sallah ba, a maimakon haka zai aiko mana da kuɗin sayayyar kayan sallar.”

Sadiya ta ce ta samu labari a cikin garinsu cewa mafarautan na cikin hatsari, kafin daga baya a sanar da ita labarin kisan ɗan nata.

Sadiya ta ce ƴaƴansu ba ɓarayi ba ne, ba kuma masu aikata laifi ba ne.

“Ƴaƴanmu ba ɓata-gari ba ne, ba su taɓa yin sata ba, su farauta ne da ke fafutikar neman na kansue,” kamar yadda ta bayyana a yayin da take roƙon gwamnati ta yi musu adalci.

Shida daga cikin mutanen 16 da aka kashe, ƴan asalin garin Toronkawa ne a jihar Kano.

Tun bayan faruwar lamarin, ƙauyen Torankawa na cikin alhini da jimami kan batun.

Ƙauyen ya yi fice a sana’ar farauta, inda suke amfani da sana’ar wajen gwanda ƙarfi da jaruntar mutanensu.

BBC ta ziyarci ƙauyen inda ta tattauna iyalan waɗanda suka mutu da kuma ɗaya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet