Connect with us

Featured

Kadara Da Na Mallaka Tun Kafin Na Zama Shugaban Kasa Ita Ce Har Yanzu Ba Ta Ƙaru Ba – Buhari

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kadarorin da ya mallaka tun kafin ya zama shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu 2015, su ne har yanzu ba su karu ba.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da mambobin Kungiyar Gwamnoni ta (PGF) a gidansa da ke Kaduna.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Laraba, 9 ga Afrilu, 2025, tsohon shugaban kasar ya bukaci gwamnonin da su dauki tafarkin da zai fi amfani ga ‘yan kasa. Ya ce shugabanci yana da kalubale da dama amma kuma wata dama ce, kuma lura da wadannan abubuwa zai taimaka matuka wajen ci gaban kasa.

Tsohon shugaban kasar ya nuna gamsuwa da irin ci gaban da gwamnonin jam’iyyar (APC) ke samu, tare da jaddada bukatar su ci gaba da jajircewa wajen inganta cigaban Najeriya.

Buhari ya kuma gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan gyaran da aka yi wa gidansa da ke Kaduna, duk da cewa ta waje gidan bai canza ba, amma an samu kyakkyawan ci gaba a ciki.

Ya gode wa gwamnonin bisa ziyarar da suka kawo masa, yana mai cewa ya taba aiki da da yawa daga cikinsu, yayin da wasu kuma sabbi ne a wajensa.

Shugaban PGF kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce ziyarar tasu na da nufin taya Buhari murnar bukin Eid-el-Fitr, da kuma mika godiya da girmamawa bisa gagarumin gudunmuwar da ya bayar wajen karfafa dimokuradiyya da jam’iyyar APC a Najeriya.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet