Connect with us

Featured

Naira Miliyan Hudu Na Samu A Asusun Gwamnati Lokacin Da Na Karbi Mulki – Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana kalubale da cigaban da gwamnatinsa ke fuskanta tun bayan hawansa mulkin jihar.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a ranar Litinin 14, Afrilu 2025. Lawal ya ce lokacin da ya karɓi mulki daga tsohon gwamna Bello Matawalle, Zamfara na cikin mawuyacin hali a kowane fanni — rashin tsaro, tabarbarewar tsarin ilimi, da kuma tarin bashin da ya addabi jihar.

“Lokacin da na hau mulki, Jihar Zamfara tana cikin wani hali da bazai misaltu ba. Tsaro ya tabarbare matuka, ilimi ya lalace, kiwon lafiya ya zama abinda ya zama, cigaban dan adam ma kamar babu. Wannan ne yasa na ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi da kiwon lafiya.

“Babu ruwa kwata-kwata a jihar tsawon wata biyar kafin na hau, amma cikin kwanaki uku kawai mun magance hakan. Gaskiya bashin da na gada ba zai yiwu a yarda da shi ba, amma a matsayin shugaba, dole ne na nemo mafita,” a cewar sa.

A cewar Gwamna Lawal “Lokacin da na hau mulki, bamu da ko sisi a baitul mali. Na tarar da bashi na ban-mamaki. Naira miliyan hudu kacal na tarar a asusun gwamnati. Kwamiti da takardu na nan suna nuna irin bashin da ake bin gwamnati, albashi na watanni hudu da rabi, bangaren shari’a suna bin gwamnati Naira biliyan 1.6, WAEC – biliyan 1.6, NECO – biliyan 1.4 da sauransu da dama da dole na fuskanta da kaina.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet