Connect with us

Featured

Gwamnatin Jigawa Ta Wajabta Sanya Hijabi Ga Jami’an Tsaro Mata

Gwamnatin Jihar Jigawa ta tsayar da matsaya dangane da tufafin da jami’an tsaro mata ke sakawa a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, gwamnatin ta umarci wasu kamfanoni uku masu zaman kansu wadanda ke samar da jami’an tsaro a jihar, da su ba wa matan da ke aiki a karkashinsu damar sanya hijabi yayin da suke bakin aiki.

Wannan umarni ya fito ne daga Kwamitin Zartarwa na Jihar, ta bakin Kwamishinan Yada Labarai, Sagir Musa, a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar bayan kammala taron Majalisar da aka yi a daren Talata a Press Gallery da ke gidan gwamnatin jihar a Dutse babban birnin jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa wannan mataki yana cikin kokarin gwamnatin jihar na samar da ingantaccen yanayi da kuma bai wa kowa dama musamman mata.

“Wannan shiri na ba wa jami’an tsaro mata damar sanya hijabi, kudiri ne na gwamnati, a kokarin ta na ba su ‘yanci wajen bin addininsu da al’adunsu ba tare da wata matsala ba. Kuma mataki ne da zai kara musu kwarin gwiwa da martaba a wajen aikinsu,” a cewar sa.

Kwamishinan ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne bayan kwamitin majalisar kan makarantun gwamnati, asibitoci, da kotuna ya gabatar da rahotonsa.

Ya ce, “Wadannan kamfanoni za su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki damar sanya hijabi yayin aiki, a matsayin kyautatawa ga addini da al’adu.”

“Wannan mataki yana sake tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Jigawa na goyon bayan manufofin da ke mutunta ma’aikata tare da kiyaye martabar su da al’adunsu,” in ji kwamishinan

Bugu da kari, Malam Musa ya bayyana cewa wannan umarni zai taimaka wa jami’an tsaro mata, wajen gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali da bin addininsu da al’adunsu.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet