Featured
Marwa Ya Jaddada Bukatar Yin Gwajin Kwayoyi Ga Masu Hidimar Kasa (NYSC)
Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Manjo Janar Buba Marwa (rtd.), ya sake nanata kiran da hukumar ke yi na tilasta gwajin kwayoyi ga masu hidimar ƙasa na NYSC, yana mai bayyana wannan mataki a matsayin matakin kariya, ba wai hukunci ba.
Marwa ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar ban girma da Darakta Janar na NYSC, Manjo Janar Olakunle Nafiu, tare da wasu manyan jami’an NYSC suka kai hedikwatar NDLEA da ke Abuja.
Mai Magana da Yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da ziyarar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 23 ga Afrilu, 2025.
Marwa ya ce ana fuskantar barazana mai ƙarfi game da shan miyagun kwayoyi tsakanin matasan Najeriya, kuma dole ne a ɗauki matakan rigakafi tun da wuri.
Ya ce, “Wannan ba wai doka ce da za ayi don a hukunta mutane ba, manufarmu ita ce rigakafi, kuma mu taimaka wa mutum tun kafin abin zamar masa jiki.”
Ya kara da cewa, “Binciken masana ya nuna cewa daya cikin bakwai na ‘yan Najeriya masu shekaru 15 zuwa 64 na amfani da miyagun kwayoyi. Kuma babu wani yanki a kasar nan da wannan abin shafa ba.”
A nasa martanin, Darakta Janar na NYSC ya bayyana shawarar a matsayin “kyakkyawan tunani”, inda ya yi alƙawarin duba shawarwarin na NDLEA domin aiwatarwa.
Ya kuma tabbatar da cewa NYSC za ta ƙirƙiri tsari na musamman domin bai wa hukumar damar tura kwararrun ‘yan NYSC zuwa ofisoshin NDLEA, musamman wuraren da ke da cibiyoyin jinya da shawaNYSCNYSC
A karshe ya yaba wa Marwa bisa jagorancinsa, tare da tabbatar da kudirin NYSC na ƙarfafa haɗin gwiwa da NDLEA wajen yakar sha da fataucin kwayoyi a tsakanin matasan Najeriya.
