Connect with us

Addini

Sarkin Musulmi Ya Sanar Da Ranar Farkon Watan Zhul Qha’ada

Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Talata 29 ga watan Afrilu, 2025 a matsayin ranar farko ta watan Zulki’ida 1446 bayan hijira.

Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Sanarwar ta biyo bayan rashin samun wani rahoto mai kyau daga kwamitin ganin wata na kasa da kuma kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi dangane da ganin jinjirin watan a ranar Lahadi, 27 ga Afrilu, 2025.

“Saboda haka, Litinin, 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446, yayin da Talata 29 ga Afrilu, 2025, za ta kasance a hukumance farkon Zulki’ida 1446”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi ya mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet