Connect with us

Featured

Rikicin Plateau Ya Janyowa Makiyaya Tafka Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Watanni Biyu

Tsawon watanni biyu da suka gabata, al’ummar ƙauyukan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar Filato ta yankin Arewa ta Tsakiya a Najeriya sun shiga mummunan hali saboda hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya janyi asarar rayuka da dukiyoyi, baya ga mutane da dama da suka jikkata.

Rahotannin da jaridar Daily Trust ta tattara sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai wa makiyaya a ƙananan hukumomin Bassa, Riyom, Jos ta Kudu da Mangu hari, inda bayanai ke cewa an sace dabbobi da dama tare da sanyawa wasu guba.

Ta’azzarar rikicin ne ya janyo hankulan manyan manyan shugabannin tsaro a ƙasar waɗanda suka ka ziyara jihar domin duba irin ɓarnar da lamarin ya haifar.

 

Cikin waɗanda suka kai ziyarar har da babban sufeton ‘yansandan Najeriya Kayode Egbetokun, da shugaban rundunar sojin ƙasar, Laftanar Janar Egbetokun Oloyede, da kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

 

Ɗimbin asarar da makiyaya suka tafka

 

Dangane da rikicin ne al’ummar Fulani suka bayyana damuwa kan irin asarar da suka tafka tsakanin watanni biyu, daga watan Maris zuwa Afrilu.

 

A cewar makiyaya, ‘yan bindiga ko wasu al’umma da ba’a san ko su waye ba a ƙananan hukumomi biyar da ke yankin Arewaci ko tsakiyar jihar ne suka sace ko harbe ko kuma sanyawa ɗaruruwan dabbobinsu guba.

 

Sun ƙara da cewa adadin asarar da su ka yi na dabbobi ya kai sama da Naira miliyan 300, a wani yanayi da hakan ke ƙara ta’zzara matsin tattalin arziƙi da suke ciki.

 

Kalaman shugaban MACBAN

 

Shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah(MACBAN), Ibrahim Yusuf Babayo ya shaidawa Daily Trust cewa, sun kai rahotan dukkanin harin da aka kaiwa dabbobinsu zuwa ga jami’an tsaro.

Babayo ya yi zargin cewa an baza wasu amfanin gona da aka sanyawa guba akan hanyoyin da suke kiwo domin dabbobinsu su ci, baya ga sanya guba a wuraren da dabbobin ke shan ruwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinovdcasinoholiganbetmarsbahissahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet