Featured
Sokoto: Harin Ƴan Ta’addan Lakurawa Ya Sake Kashe Mafarauta 13

Aƙalla Mafarauta 13 ake faragabr sun mutu a harin da ƴanta’addan Lakurawa suka kai kan dandazon masu bikin farauta na shekara-shekara a dajin Hurumi da ke Talewa a ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Mafarautan daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa sun tattaru a dajin na Hurumi don gudanar da bikin ranar Alhamis ɗin makon jiya, sai dai yayinda suke tsaka da shagulgulansu ƴanta’addan sun far musu da misalin ƙarfe 1 na rana kodayake dama mahukuntan jihar sun gargaɗesu game da haɗarin wannan biki saboda matsalolin tsaro a yankin.
A cewar wasu majiyoyi Mafarautan waɗanda ke riƙe da bindigogin gargajiya da kuma karnukansu kai tsaye sun kutsa kai cikin dajin inda a nan ne ƴan ta’adda ke da sansani.
Wani mazaunin garin Tangaza da ya nemi a sakaya sunansa ya ce zuwa yanzu an iya ɗakko gawarwakin Mafarautan 3 amma ba a iya gano 10 daga ciki ba, kodayake wasu da suka tsira da rayukansu sun dawo gida.
A cewar majiyoyi, garin Kangiye ya yi asarar Mafarauta 5 yayinda a garin Chancha Mafarautansu 2 suka mutu a harin sai kuma wasu ƙarin biyu daga garin Rantijadi kana wani Mafarauci guda daga Gidan Kaji da kuma wani ƙarin 1 daga Gandaba Yamma sannan wasu guda biyu daga Gandaba Gabas.
Wasu majiyoyi sun ce ƴan ta’addan sun so amfani da Mafarautan don janyo hankalin jami’an tsaro waɗanda tun farko sune suka nufaci kashewa saɓanin ƴan Farautar.