Featured
Hukumar CREDICORP Za Ta Baiwa Yan Najeriya Bashi Mara Kudin Ruwa

Hukumar bayar da bashi ta Nigerian Consumer Credit Corporation (CREDICORP), wacce aka samar karkashin shirin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na Renewhope, ta kaddamar da shirinta na wayar da kan al’umma kan amfani da rance wajen samun kayayyakin more rayuwa.
Taron kaddamar da shirin ya gudana ne a yau laraba 21 ga watan mayu 2025, a rufaffen dakin taro na Filin Wasa Na Sani Abacha Stadium da ke Kofar Mata a jihar Kano.
Hukumar ta ce zabi kaddamar da wannan shiri a Jihar Kano ne kasancewarta cibiyar kasuwanci a fadin Najeriya, ta kuma ce babban makasudin wannan taron shi ne don wayar da kan al’umma musamman yan Arewacin Najeriya game da muhimmanci da kuma amfanin wannan rance mara kudin ruwa domin inganta rayuwar yan Najeriya.
Daga cikin abubuwan da hukumar ke bayarwa rance akwai: Solar, Mota, Firinji, Babur, Wayar hannu, Computer, Gida da dai sauran su.
Kazalika hukumar ta ce wannan bashi za a dinga biya ne da kadan-kadan ba tare da an karawa mutum ko sisi ba.
A yayin gudanar da taronm, Shugaban Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Musa Umar Arzai, ya jadadda goyon bayan sa game da wannan bashi, ya kuma ce da yawan mutane suna son wannan bashi, amma rashin sanin hanyoyin da za su bi wajan samun sa shi ya ke ba su wahala.
A karshe Arzai ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen wayar da kan al’umma dangane da muhimmancin wannan bashi, domin su ma su amfana kamar yadda takwarorin su na kudancin Najeriya suka ci gajiyar tsarin tun farko.