Featured
Shugaba Tinubu Ya Bukaci A Kawo Karshen Take Hakkin Yara A Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da kudirinsa na kare hakkoki da jin dadin yara a Najeriya, inda ya bayyana su a matsayin “ginshiki na makomar Najeriya” a cikin jawabin da ya yi don bikin Ranar Yara ta Duniya ta shekarar 2025.
A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Talata 27 ga Mayun 2025, Shugaban ya jaddada bukatar hadin kai don yaki da tashin hankali da kuma sakacin da ke shafar miliyoyin yara a fadin kasar.
Tinubu ya kuma bayyana wasu muhimman shirye-shirye don karfafa tsarin kariyar yara, inganta hanyoyin koyo cikin kwanciyar hankali, da kuma tabbatar da cewa babu wani yaro dan Najeriya da za a bari a baya.
Shugaban ya kuma yi kira ga iyalai, makarantu, al’ummomi, da gwamnati da su hada hannu wajen gina Najeriya.