Featured
Gwamnatin Neja Za Ta Haɗa Kai Da Matatar Ɗangote Domin Haƙo Ɗanyen Man Jihar

Gwamnan jihar Neja Umar Bago, na son yin aikin haɗin gwiwa da matatar man fetur ta Dangote domin haƙowa da kuma hada-hadar ɗanyen mai da aka gano a Tekun Bida da ke jihar.
Umar Bago ya bayyana aniyar gwamnatin tasa ne yayin wani jawabi da ya yi a bikin baje-kolin kasuwanci da aka gudanar a Minna babban birnin jihar a ranar Lahadi 01 ga Yunin 2025.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa kamfanin na Dangote ne ya ɗauki nauyin bikin.
Gwamnan ya siffanta albarkatun ɗanyen man da aka gano jihar na da shi a matsayin tikitin “cigaban tattalin arzikin Neja”.
NAN ya ruwaito cewa wani bincike da aka gudanar a 2023 ne ya gano rijiyoyin mai 17 da za a yi kasuwancinsu a jihar, inda aka ƙiyasata cewa za a iya kasuwancinsa na tsawon shekara 70.