Connect with us

Featured

Sojojin Najeriya Za Su Fara Amfani Da Kayan Tsaro Na Cikin Gida Saɓanin Na Waje – Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sannu a hankali Najeriya na shirin daina dogaro da kayan sojoji daga waje zuwa samar da su a cikin gida.

A cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman akan Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a, Mati Ali, ya rabawa manema labarai ranar Laraba 04 ga Yuni 2025, Badaru ya ce “wannan zai taimaka wajen samar da kayan sojoji, gyara, sabunta, da kuma samar da kayan yaƙi a cikin gida.”

A cewar ministan, wannan mataki na dogaro da kayan cikin gida babban ci gaba ne wajen samun ‘yancin kai domin ƙarfafa tsaro a fadin ƙasar.

Badaru ya bayyana haka ne bayan kammala ziyarar kwanaki biyu da ya kai ga cibiyoyin sojoji da masana’antu a Kaduna.

Ministan ya kai ziyara ga muhimman cibiyoyin sojoji, ciki har da Makarantar Koyon Soja ta Najeriya (NDA), Kamfanin Gine-ginen Sojoji na Najeriya (Command Engineering Depot), Kamfanin Buffalo Engineering Technical Services Limited, da kuma Cibiyar Fasahar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF Institute of Technology).

A lokacin ziyarar, Badaru ya yaba da ci gaban da ake samu wajen horar da ma’aikata, samar da kayan aiki na cikin gida, da gyaran kayan yaƙi.

A karshe ministan ya yabawa jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen sauya fasalin harkar tsaron Najeriya, inda ya yaba da amincewar shugaban kasa game da dokar kafa Kamfanin Kera Kayan Yaƙi na Najeriya (Defence Industries Corporation of Nigeria) a matsayin doka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet