Featured
Matsalar Ruwa Ta Kusa Zuwa Ƙarshe A Jihar Kano – Doguwa
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na shawo kan matsalar karancin ruwan sha da ke addabar wasu yankuna a fadin jihar.
Kwamishinan Ruwa na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan a lokacin wata ziyarar duba aikin da ya kai a matatar ruwan Joda, da ke Karamar Hukumar Gabasawa.
Sanarwar hakan ta fito ne a jiya talata 24 ga Yuni, 2025. Daga bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Yankin Gezawa, Jamilu Mustapha Yakasai.
A cewar Kwamishinan, gwamnati ta samar da sabon injin tura ruwa daga madatsar ruwa ta kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa, da kuma wasu sassan unguwannin nasarawa da ‘yan Kaba, inda ya ce wannan mataki wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar don tabbatar da wadataccen ruwan sha ga al’ummar da abin ya shafa.
Kazalika yace Hukumar samar da ruwa a jihar Kano tana ci gaba da gyare-gyare a sauran matatun ruwa domin kara inganta hanyoyin samar da ruwan sha a fadin jihar.
Kwamishinan ya kuma tabbatar wa da mazauna yankunan da suka fi fuskantar matsalar cewa nan ba da jimawa ba za su fara ganin sauyi wajen samun ruwan sha mai tsafta.
Doguwa ya ce gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na daukar wannan aiki da matukar muhimmanci domin saukaka wa jama’a rayuwa da kuma inganta lafiyar su.
