Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Fara Horas da SSR Da SR 132 Domin Inganta Hanyoyin Sadarwa Tsakanin Gwamnati Da Al’ummah

Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano ta shirya wata horaswa ta tsawon kwanaki hudu ga Masu Rahoto na Musamman (SR) da Manyan Masu Rahoto na Musamman (SSR) domin inganta hanyoyin sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.

Taron wanda yake hadin gwiwa ne da Cibiyar Horas da Ƴan jarida ta Ƙasa da kuma Ausam Communication an fara gudanar da shi a ranar Litinin 07 ga Yuli 2025, a dakin taro na Dangote Business School da ke Sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano.

Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, na daga cikin wadanda su ka halarci taron, inda Shugaban Ma’aikata Abdullahi Musa ya wakilce shi, sai Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, da Daraktan Cibiyar Horas da Yan Jaridu ta Ƙasa da kuma Ƴan jaridu.

Da yake jawabi a wajen bikin bude taron, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa an tsara horon ne domin koyar da sabbin dabarun sadarwa na zamani ga mahalartan su 132, domin su iya tallata manufofi da nasarorin Gwamnatin Jihar Kano yadda ya dace.

Kwamishinan ya ce kafin yanzu ma’aikatarsa ta riga ta gudanar da irin wannan horo ga jami’an yada labarai na kananan hukumomi, domin tabbatar da isar da sakon gwamnati zuwa kowane sako na jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Malam Abdullahi Musa, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa kokarin SSRs da SRs, yana mai bayyana su a matsayin ginshikan yada sahihan bayanai a cikin gwamnatin jihar.

Malam Musa ya tunatar da mahalarta cewa tsarin nada SSRs da SRs na daga cikin sabbin dabarun da Gwamna Yusuf ya kirkiro domin tabbatar da ingantacciyar hanya wajen isar da sakon gwamnati.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet