Featured
Ahmad Musa Ya Musanta Batun Bayar Da Motoci Ga Ƴan Wasan Pillars

Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya raba motocin alfarma ga ‘yan wasa da jami’an kulob ɗin Kano Pillars bayan nadin sa a matsayin babban manajan kulob ɗin.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata 08 ga Yuli, Musa ya bayyana rahotannin da ke yawo a matsayin ƙarya da yaudara.
Jita-jitar da ta fara yaduwa tun da safe ta ce Musa ya bai wa dukkan mambobin tawagar Kano Pillars da masu horas da su sabbin motocin Land Cruiser a matsayin alamar dawowarsa da jagoranci a kulob ɗin.
Da yake mayar da martani, Musa ya ce labarin ba gaskiya bane, kuma ya bukaci jama’a da kafafen watsa labarai da su rika tantance bayanai daga sahihan tushe kafin yadawa.
“Na samu labarin cewa ana yaɗa ƙarya cewa na raba motoci ga ‘yan wasa da jami’an kulob ɗin Kano Pillars bayan nadin da aka yi mini a matsayin babban manajan kulob ɗin. Wannan ikirari ba gaskiya ba ne ko kaɗan.” Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.
“Ina kira ga jama’a, kafafen yada labarai, da masu amfani da kafafen sada zumunta da su rika tantance gaskiyar duk wani labari kafin su yada shi. Yaɗa labaran ƙarya ba wai kawai yana ruɗar da jama’a ba ne, har ma yana ɓata sunan kulob ɗin da shugabancinsa,” in ji shi.
A karshe ya bayyana cewa burinsa shi ne farfaɗo da martabar kulob din nasa.