Featured
Mutane 2 Sun Rasu, 10 Sun Jikkata Sanadiyyar Hadarin Mota a Jigawa
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu goma, a wani haɗarin mota da ya faru a kan hanyar Ringim-Kano, cikin ƙaramar hukumar Ringim a jihar Jigawa.
Kwamandan hukumar a jihar, Umar Mas’ud, ya shaida wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Juma’a 11 ga Yuli, 2025, cewa haɗarin wanda ya haɗa da motoci biyu na Volkswagen, ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a.
Mas’ud ya ce mutane 13 ne gaba ɗaya suka shiga cikin haɗarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 10:40 na safiyar ranar Alhamis 10 ga aYuli, 2025.
Kwamandan ya ƙara da cewa dukkan mutanen da abin ya shafa ‘yan ƙauyen Bareda ne daga ƙaramar hukumar Ikara a jihar Kaduna.
Mas’ud ya bayyana cewa hukumar ta FRSC ta gano kuɗi har Naira miliyan biyu da dubu ɗari shida da sittin da shida (N2,166,700) da ke hannun ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu da kuma wani da ya tsira.
Ya ce an miƙa kuɗin ga dangin waɗanda abin ya shafa a gaban DPO na yankin, ASP Abdullahi Ibrahim.
Ya ka yaba da jajircewar ma’aikatan rundunar da ke kula da yankin wajen gaskiya da amana wajen gano kuɗin da kuma miƙa shi ga masu shi.
