Featured
Gwamnatin Kano Ta Fara Bincike Kan Mutuwar Wasu Ɗalibai a Sakandiren Bichi
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Ali Makoda, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wasu dalibai guda biyu a makarantar Government Boarding Secondary School, Bichi.
Rahotanni sun bayyana cewa daliban da suka mutu, Hamza Tofawa da Umar Dungurawa, sun samu rauni sakamakon wani hari da wasu daliban makarantar suka kai musu inda su ka yi amfani da wani irin ƙarfe da ake kira “Gwale-Gwale”.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Kiru, ya rabawa manema labarai a ranar Laraba 16 ga Yuli, 2025.
A cewar sanarwar, Kwamishinan Ilimi, ta bakin Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Bashir Muhammad, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa kowa ya samu hakkinsa.
“Rahotanni sun nuna cewa wannan aika-aikar ta biyo bayan wani hukunci ne da wasu manyan dalibai suka ɗauka da kansu don ladabtar da waɗanda suka mutu, bisa zargin sun aikata wani laifi,” in ji shi.
Sakataren Dindindin wanda ya ziyarci makarantar tun kafin fitar da sanarwar, ya shawarci dalibai da su rika zama masu hankali tare da guje wa ɗaukar doka a hannunsu.
“Ya kamata ku guji ɗaukar doka a hannunku, ku tabbatar da kai kowacce irin matsala ga hukumomin makaranta domin su ɗauki mataki da ya dace,” a cewarsa.
Ya kuma bayyana ta’aziyya ga iyalan mamatan, inda ya ce: “A madadin Gwamnatin Jihar Kano, Ma’aikatar Ilimi da al’ummar Kano, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda su ka rasu , tare da addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus.”
Wadanda aka kai wa harin sun hada da Hamza Idris mai shekara 19 daga ajin SS3B, Umar Yusuf mai shekara 18 daga SS2C, Ibrahim Ibrahim daga SS2B, da Aliyu M. Nasir daga SS2C.
“Daga bisani, an tabbatar da mutuwar Idris da Yusuf a Asibitin Gwamnati na Bichi, yayin da Ibrahim da Nasir ke ci gaba da samun kulawar likitoci.
