Featured
Yan Kasuwa Sun Koka Yayin Da Dangote Ke Shirin Rage Farashin Gas Ɗin Girki

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirinsa na rage farashin gas ɗin dafa abinci (LPG) domin ya zama mai sauƙin samu ga talakawa. Ya kuma yi barazanar fara siyar da shi kai-tsaye ga masu amfani da shi idan ‘yan kasuwar gas suka ƙi saukar da farashin.
Sai dai, masu ruwa da tsaki a harkar sun nuna rashin amincewa da wannan mataki, suna zargin cewa Dangote na shirin mallakar kasuwar LPG gaba ɗaya. A cewarsu, hakan zai jefa sauran ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da wasu baƙin cikin gida da na ƙasashen waje suka kai masa ziyara a matatar mai da ke Lekki, inda ya bayyana cewa farashin gas ɗin dafa abinci ya yi tsada matuƙa kuma bai dace da rayuwar yawancin ‘yan Najeriya ba, musamman waɗanda ke amfani da itace don girki.
Ya bayyana cewa matatar Dangote yanzu tana samar da ton 22,000 na LPG a kullum, kuma ana ƙara yawan samarwa domin rabawa a Najeriya, musamman a daidai lokacin da ake ƙarfafa amfani da gas don girki.
A cewarsa: “ A yanzu haka, muna samar da ton 2,000 na LPG a kullum. Najeriya na tafiya a hankali zuwa amfani da LPG, amma farashin ya yi tsada. Yanzu muna kokarin rage farashin domin ya kasance mai sauƙi.”
Dangote ya ce: “Idan ‘yan kasuwa ba su rage farashin ba, to za mu fara siyarwa kai tsaye ga jama’a, domin su daina amfani da itace da fetur wajen girki.”
A yanzu, farashin LPG yana tsakanin N1,000 da N1,300 duk kilo. Dangote ya ce za a rage wannan farashi sosai domin ya zama mai sauƙin samu.
Sai dai wasu daga cikin masu kasuwancin gas din sun nuna rashin jin daɗi da wannan yunkuri na Dangote.
Tsohon Shugaban Rukuni na LPG da Gas ɗin Cikin Gida na Ƙungiyar Kasuwanci ta Legas, Mista Godwin Okoduwa, ya bayyana wannan shiri a matsayin wani yunƙuri na monopoly — mallakar kasuwa ta mutum ɗaya.
Ya ce kamata ya yi a ci gaba da bin hanyar haɗin gwiwa domin ci gaba, kamar yadda aka yi daga 2007 zuwa 2022, inda kasuwar LPG ta tashi daga ton 70,000 zuwa sama da ton miliyan 1.3.
“Ba za a samu ci gaba ta hanyar mallakar kasuwa da mutum ɗaya zai yi ba. A yau, Najeriya tana da ƙasa da 6kg na LPG per capita, amma ƙasashe kamar Afrika ta Kudu, Morocco da Tunisia sun wuce hakan da nisa,” in ji shi.
Ya ce Dangote bai kamata ya takura wa ‘yan kasuwa da suka riga suka kafa tushe a kasuwar LPG ba.
“Ya kamata a samu haɗin gwiwa, ba faɗa ba. Dole ya mutunta kasuwar da ya samu a buɗe, kuma mu haɗa kai don bunƙasa ta.