Connect with us

Featured

Ganduje Yana Landan Ziyarar Aiki – Muhammad Garba

Tsohon Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin da yasa bai samu halartar ziyarar ta’aziyyar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Kano a ranar Juma’a 18 ga Yuli ba, inda ya ce hakan ya faru ne sakamakon wata muhimmiyar tafiya zuwa birnin London.

Wannan ziyara an shirya ta ne kwanaki biyar bayan Ganduje ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Tsohon Babban Sakataren Ganduje lokacin yana shugaban jam’iyya, Malam Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Asabar 19 ga Yuli, 2025.

Garba ya ce, sabanin jita-jitar da ke yawo a kafafen yada labarai da ke nuni da cewa ko dai Ganduje na fama da rashin lafiya ko kuma an ware shi daga jerin mutanen da za su raka shugaban kasa, tsohon shugaban jam’iyyar ya tafi London ne tun da dadewa domin wata ganawa ta kashin kai da aka tsara tun kafin wannan lokaci.

Ya ce an sanar da Ganduje game da ziyarar Shugaba Tinubu zuwa Kano domin gaisuwar rasuwar fitaccen attajiri da hamshakin dan kasuwa, marigayi Alhaji Aminu Dantata, amma duk da kokarinsa na sauya jadawalin tafiarsa da dawowa cikin lokaci, ba a samu damar gyara tsare-tsaren tafiyar ba.

Garba ya jaddada cewa murabus din Ganduje daga shugabancin APC bai shafi dangantakarsa ta kut-da-kut da Shugaban kasa Tinubu ba, wacce aka gina bisa girmamawa da fahimtar juna ta fuskar siyasa tun shekaru da dama da suka gabata.

 

 

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet