Featured
Jihohin Najeriya 12 Sun Ware Naira biliyan 102 Domin Gyaran Gidan Gwamnati Da Sayen Motocin Alfarma

Akalla jihohi 12 a Najeriya sun ware kimanin naira biliyan 102 a kasafin kudinsu na shekarar 2025 domin gyaran gidajen gwamnati da ofisoshi, da kuma sayen sabbin motoci irin na alfarma (SUVs), kamar yadda binciken jaridar Sunday PUNCH ya nuna.
Kudaden sun hada da zamanantarwa da gyare-gyare na gidan gwamnati da kuma dakunan baƙi na manyan baki, tare da sayen motoci da dama, ciki har da Toyota Prado SUVs, Jeep, Hilux pickups, Camry, da Corolla.
Wadannan kudade suna cikin kudaden kashewa na manyan aiyuka (capital expenditure) da aka fitar a rahotannin yadda aka gudanar da kasafin kudin watanni ukun farko na 2025 daga shafukan yanar gizon jihohin.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da:
Lagos, Adamawa, Borno, Cross River, Delta, Ekiti, Imo, Jigawa, Kebbi, Ondo, Taraba da Yobe.
Bayanin wasu daga cikin jihohin:
Lagos State
Ta ware kusan N33bn gaba ɗaya.
N20.67bn don motoci ga ‘yan majalisa.
N11.04bn don gyaran ginin majalisar dokoki.
N150m don gyaran gidan shugaban majalisa da gidan baƙi.
N1.15bn don gyaran lodges a Alausa da Abuja.
Delta State
N14.91bn gaba ɗaya.
N11.23bn don siyan motoci 260 ciki har da SUVs.
N2.73bn don gyaran gidajen gwamnati a Asaba, Warri, Abuja, da Lagos.
N220m don kula da dakunan baƙi na VIP.
Taraba State
N9.57bn aka ware gaba ɗaya.
N3bn don gyaran gidajen gwamnati a ƙananan hukumomi.
N2.4bn don gyaran gidan gwamnati da lodges a Jalingo.
N800m don lodge a Yola.
N650m don gidan baƙi na shugaban ma’aikata.
Borno State
N7.75bn gaba ɗaya.
N6.92bn don siyan motoci 50.
N830.5m don lodges, gami da N500m don gine-ginen ma’aikata 60.
Ondo State
N7.51bn gaba ɗaya.
N3.95bn don motoci ga ‘yan majalisa.
N2bn don motocin gwamnati masu kariya.
N1.33bn don gyaran gidajen gwamnati da ofisoshi.
Adamawa State
N6.46bn.
N2.9bn don motoci 42.
N3.56bn don gyaran gidajen gwamnati a Yola da Abuja.
Kebbi State
N5.66bn.
N2.36bn don motoci ga majalisa.
N3.3bn don gyaran ofisoshi a Abuja, Lagos, Kaduna da Sokoto.
Ekiti State
N5.16bn.
N2.36bn don gyaran lodges.
N3bn don motoci, ciki har da Prado da JAC SUVs.
Cross River State
N4.52bn.
N1.5bn don gyaran gidan gwamnati da dakunan baƙi.
N900m don Presidential Lodge a Calabar.
N1.39bn don Prado SUVs ga ‘yan majalisa.
Jigawa State
N3.39bn gaba ɗaya.
N300m don gyaran gidan baƙi.
N1bn don Hilux guda 4.
N1.14bn don motoci ga ma’aikata da jami’an gwamnati.