Featured
Gwamnatin Jigawa Ta Biya Naira Biliyan 1.5 Ga Masu Ritaya 569
Hukumar Kula da Tsarin Fansho na Ma’aikatan Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi ta bayyana cewa ta fitar da fiye da Naira biliyan 1.5 domin biyan hakkokin masu ritaya 569 a fadin jihar.
Sakataren zartarwa na hukumar, Dr. Binyaminu Shitu, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Litinin 28 ga Yuli, a Hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, jimillar kudin da za a raba ga wadanda suka amfana ya kai Naira 1,505,449,327.78, wanda ya hada da nau’o’in biyan hakkoki daban-daban kamar kudin ritaya, hakkokin rasuwa, da kuma saura daga fanshon wadanda suka rasu.
Dr. Shitu ya bayyana cewa daga cikin wadanda suka ci gajiyar kudaden:
Mutane 287 sun fito daga ma’aikatan gwamnatin jiha,
158 daga kananan hukumomi,
124 daga ma’aikatan hukumar ilimi ta kananan hukumomi (LEA).
Ya kara da cewa: An ware Naira 875,625,045.00 ga wadanda suka fito daga ma’aikatan jiha,
Naira 355,025,795.72 ga ma’aikatan kananan hukumomi,
Sai kuma Naira 274,798,487.06 ga ma’aikatan LEA.
Sakataren ya kara jaddada cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen biyan hakkokin ma’aikata a kan lokaci, musamman biyan fansho a makon farko na kowane wata, tare da yabawa kokarin gwamnatin jihar na inganta walwalar ma’aikata da masu ritaya.
Ya ce tsarin fanshon jihar Jigawa yana daga cikin mafi kyau a kasar nan, inda sama da jihohi ashirin suka ziyarci jihar domin koyon dabarun gudanarwa daga gare ta.
