Connect with us

Featured

Jam’iyyar SDP Ta Kori El-Rufai, Ta Haramta Masa Shiga Jam’iyyar Na Tsawon Shekara 30

Kwamitin Zartarwa na Kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya kori tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, daga cikin jam’iyyar tare da hana shi hulɗa da jam’iyyar a kowane mataki na tsawon shekara 30.

Jagororin jam’iyyar sun zargi El-Rufai da yin ƙarya da cewa ya shiga jam’iyyar, da kuma ƙoƙarin rikita jam’iyyar ta hanyar aikata ayyukan da su ka saɓa doka da kokarin kawo rudani a siyasance

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Kasa na jam’iyyar, Araba Aiyenigba, ya fitar a 28 ga Yuli, 2025.

A cewar jam’iyyar, bayan bincike mai zurfi da suka gudanar kan ikirarin El-Rufai na zama ɗan jam’iyyar da kuma zarge-zargen da suka shafi aikatawa ta bayan fage da ke haifar da rabuwar kawuna, an yanke hukuncin kora bisa dokar jam’iyyar.

Sanarwar ta ce: “El-Rufai bai yi rajista da SDP a matakin unguwarsu ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada, amma sai ya wallafa a kafafen sada zumunta cewa ya shiga jam’iyyar. Har ma ya ƙirƙiri takardu na bogi yana ikirarin zama ɗan jam’iyyar, ya ɗauki hoto tare da wasu shugabannin jam’iyyar da aka dakatar domin ƙarfafa wannan ƙarya.”

Jam’iyyar ta ce El-Rufai ya nemi a shirya masa liyafar tarba a ofishin jam’iyyar na kasa a Abuja, amma an bukace shi da ya je unguwarsu ta Unguwar Sarki a Kaduna North ya yi rajista kamar yadda doka ta tanada.

SDP ta kara da cewa El-Rufai ya: Gaza yin rajista da jam’iyyar a mazabarsa. Sannan ya yi ƙarya da hotuna da wasu shugabannin jam’iyyar domin ya nuna cewa ya shiga jam’iyyar. Bugu da kari ya yi amfani da sunan jam’iyyar da tambarinta ba tare da izini ba.

Jam’iyyar ta ce: “Bayan tabbatar da cewa El-Rufai ya bayyana kansa a bainar jama’a a matsayin ɗan ADC, kuma yana ci gaba da aikata abubuwa masu sabawa ka’idojin SDP, jam’iyyar ba ta da wani zabi illa ta raba kanta da shi gaba ɗaya.”

“Saboda haka, an haramta masa shiga jam’iyyar ko hulɗa da sunanta, tambarinta, ko ayyukanta na tsawon shekara 30, daga yau.”

 

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet