Connect with us

Featured

NNPC Ya Ƙaryata Jita-jitar Sayar da Matatar Mai ta Port Harcourt

Kamfanin Man Fetur na Najeriya, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPC Ltd), ya karyata rade-radin da ke yawo kan cewa zai sayar da Matatar Mai ta Port Harcourt, yana mai jaddada cewa yana da cikakken kudiri na kammala gyaran matatar da kuma ci gaba da rike ta a hannun gwamnati.

Darakta Janar na Kamfanin, Bashir Bayo Ojulari, ne ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani tsakanin ma’aikata da shugabannin kamfanin da aka gudanar a hedikwatar kamfanin dake Abuja a ranar Talata 29 ga Yuli, 2025.

Ojulari ya ce, sakamakon bincike da ake ci gaba da yi ya nuna cewa matakin da aka yi niyyar dauka a baya, na fara amfani da matatar Port Harcourt kafin kammala gyaran ta gaba daya, ba shi da tushe kuma ba zai haifar da riba ba.

Duk da cewa ana samun ci gaba a gyaran matatun ukun, akwai bukatar yin hadin gwiwa da kwararru na fasaha domin kammala gyaran Port Harcourt cikin kwarewa da inganci.

Saboda haka, sayar da matatar ba zaɓi bane da ke kan tebur yanzu, domin hakan zai haifar da ɗa-mai-ido-ba.

Wannan sanarwa na zuwa ne bayan rahotanni da suka bulla sakamakon wata hira da Ojulari ya yi da Bloomberg a taron OPEC na shekarar 2025 da aka yi a Vienna, Austria, inda ya ce “duk wani zaɓi na kan tebur ne.” Wannan ya tayar da kura kan makomar matatun Najeriya.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet