Featured
Za a Fara Yiwa Ɗaliban Jami’a Gwajin Miyagun Ƙwayoyi – Ministan Ilimi

Ministan Ilimi a Najeriya Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnati za ta fara aiwatar da gwajin kwayoyi na dole da kuma bazata ga ɗaliban makarantu na gaba da sakandire a fadin ƙasar.
Wannan matakin ya biyo bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Janar Buba Marwa (mai ritaya), a birnin Abuja a ranar Laraba 30 ga Yuli, inda suka tattauna hanyoyin dakile amfani da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da ɗalibai.
A cewar wani bayani da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, Ministan ya amince da bukatar sauya tsarin karatun makarantun sakandire domin saka sabon darasi kan ilimin illolin miyagun kwayoyi. Haka kuma, an yanke shawarar kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar ilimi da NDLEA don gudanar da aikin.
Marwa ya gabatar da tsari mai matakai uku:
1. Sauya abun da ke cikin litattafan koyar da ilimin miyagun kwayoyi a makarantu.
2. Wayar da kan daliban sakandire kai tsaye akan illolin kwayoyi.
3. Da kuma aiwatar da dokar gwajin kwayoyi a manyan makarantu — ga sabbin ɗalibai, waɗanda suka dawo daga hutun makaranta da kuma gwaje-gwajen bazata.
Marwa ya bayyana cewa matsalar shan kwayoyi barazana ce ga tsaron ƙasa da ci gaban matasa, yana danganta ta da laifuka irin su ta’addanci da ‘yan bindiga.
Ya ce, “Muna fafutukar ceton rayuwar ‘ya’yanmu. Da babu kwayoyi, da yawancin laifukan da ake aikatawa ba za su yiwu ba.”
A nasa bangaren, Ministan Ilimi ya jaddada muhimmancin magance matsalar, yana cewa, “Idan matasa suka fada cikin shan miyagun kwayoyi, ba za su rika zuwa makaranta ba. Ko da sun je, ba za su samu ilimi mai amfani ba.
“A karshe me ke faruwa? Basirar tunani da fahimtarsu kan ragu sosai. Daga nan sai su zama wadanda ba su da amfani a kasuwa. Kuma hakan na jefa su cikin kangin talauci da zaman banza.”
Ministan ya tabbatar da cewa za a fara gwajin kwayoyi ga sabbin ɗalibai da kuma waɗanda suka dawo, a duk jami’o’i da manyan makarantu.
Ya ce: “Ka kuma ambaci batun gwajin kwayoyi a manyan makarantu, kuma da gaske ne. Za mu yi shi. Dole ne mu yi shi. Ba mu da wani zabi. Za mu fara da jami’o’i — sabbin ɗalibai, waɗanda suka dawo da kuma na bazata.”
Ya sanar da kafa Sashen Dakile Amfani da Miyagun Kwayoyi a cikin ma’aikatar ilimi, tare da tabbatar da cewa ana sake duba tsarin karatun sakandire domin sabunta shi.