Connect with us

Featured

Gwamnatin Jihar Kano Ta Karɓi Rahoton Kwamitin Binciken Kwamishinan Da Ake Zargi Da Belin Dillalin Miyagun Kwayoyi

Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin tantance zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na Jihar, Alhaji Ibrahim Namadi, dangane da rawar da ya taka wajen samun beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin 04 ga Agusta, 2025.

A yayin mika rahoton ga Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Alhaji Umar Farouk Ibrahim, Shugaban kwamitin kuma mai ba Gwamna shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki, Barista Aminu Hussain, ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike mai zurfi, cikin gaskiya da bin hujjoji.

“Mun yi hira da Kwamishinan, wanda shi ma ya mika bayanin sa a rubuce. Mun kuma tuntubi wasu muhimman mutane da ke da alaka da batun, ciki har da Abubakar Umar Sharada, Mai taimakawa Gwamna kan Siyasa, da Musa Ado Tsamiya, Mai taimakawa Gwamna kan Hanyoyin Ruwa,” in ji Barista Hussain.

Ya ƙara da cewa kwamitin ya tuntubi hukumomin tsaro da na doka, ciki har da Hukumar Tsaro ta SSS, Hukumar NDLEA, da kuma Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), domin tabbatar da ingancin binciken.

“Mun duba takardun da aka tabbatar da sahihancinsu (CTCs) tare da nazarin dokokin da suka shafi al’amarin. Binciken ya gudana cikin gaskiya, bin ƙa’ida, da bin ka’idojin aikin lauya,”.

Barista Hussain ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kin tsoma baki da ya yi a aikin kwamitin, yana mai cewa hakan ya nuna irin salon shugabanci na gaskiya da girmama doka da tsarin mulki.

“Muna godiya ƙwarai ga Mai Girma Gwamna bisa yadda ya bar kwamitin ya gudanar da aikinsa cikin ‘yanci. Wannan ya ƙarfafa mana gwiwa ba tare da tsoro ko son rai ba,” in ji shi.

A nasa bangaren, SSG Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana godiyarsa ga kwamitin bisa yadda suka gudanar da aikin cikin kwazo da kwarewa.

“Bari in mika godiya ta musamman ga shugaban kwamitin da mambobinsa saboda ƙwazonku da sadaukarwar da kuka nuna a wani batu da ya ja hankalin al’umma,” in ji Farouk.

Ya kuma jaddada amincewar gwamnati da kwamitin bisa yadda suka yi aikin cikin gaskiya duk da matsin lamba daga jama’a.

“Dukkanin jama’a sun amince da kwarjinin ku. Kun kammala aikin a cikin lokacin da aka diba. Ina tabbatar muku da cewa cikin sa’a guda, wannan rahoto zai isa hannun Mai Girma Gwamna domin nazari da ɗaukar mataki da ya dace,” in ji shi.Ana sa ran Gwamnatin Jihar Kano za ta yi nazari a kan rahoton da ta karɓa, sannan ta ɗauki matakin da ya dace bisa shawarwarin da ke cikinsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetjojobetcasibomcasibommatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantgrandpashabetcasibomnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet