Connect with us

Featured

Akwai Yiwuwar Samun Ambaliyar Ruwa a Jihohin Najeriya 19 – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargaɗi game da matsanancin ruwa da za a fuskanta na tsawon kwana biyar wanda zai iya haddasa ambaliya a wurare 76 da ke cikin jihohi 19.

Wannan gargaɗi ya fito ne daga Cibiyar Hasashen Ambaliya ta Ma’aikatar Muhalli, inda aka nemi al’umma da hukumomi su dauki matakan gaggawa don kaucewa mummunar barna.

Jihohin da ke cikin haɗarin ambaliya sun hada da:

Kudu maso Kudu: Akwa Ibom, Cross River, Delta, Edo

Arewa maso Gabas: Bauchi, Gombe, Borno, Taraba, Yobe

Arewa maso Yamma: Kebbi, Sokoto, Katsina, Zamfara

Arewa ta Tsakiya: Niger, Benue, Nasarawa, Kaduna, Plateau

Kudu maso Yamma: Ogun, Lagos

Kudu maso Gabas: Anambra, Ebonyi, Imo

Babban Birnin Tarayya: Abuja

A baya bayan nan dai, ambaliya ta kashe mutane 191, yayin da mutane 94 su ka bata, kuma fiye da 134,000 ne lamarin ya rutsa da su a 2025.

Jihohin da suka fi fuskantar hasara: Niger (mutum 163 sun mutu), Adamawa (mutum 26).

Gidaje 9,499 da gonaki 9,450 ne su ka lalace.

Maza 27,121, mata 41,539, yara 60,071, da tsofaffi 5,704 ne suka fi shan wahala.

Masana dai sun ja hankalin gwamnati da al’umma cewa sai an zuba jari sosai, sannan an gyaran tituna, magudanun ruwa, da wayar da kan jama’a matukar ana son daƙile yiwuwar faruwar wannan ambaliya, don haka ya kamata jama’a su dauki matakan kariya tun da wuri.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet