Featured
Gidauniyar Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF) ta yi Kira ga Gwamnatin Jihar Kano Kan Albashin Ma’aikatan Hisbah

Gidauniyar Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF), karkashin jagorancin Ambassador Auwalu Muhd Danlarabawa, ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da ta yi duba kan albashin ma’aikatan hukumar Hisbah, tare da daukar matakin kara musu albashi domin inganta rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan tsaro da addini a cikin al’umma.
Ambassador Danlarabawa ya jaddada cewa ma’aikatan Hisbah suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro, kare tarbiyyar al’umma da kyautata zamantakewa, don haka yana da muhimmanci gwamnati ta kula da hakkokinsu da walwalarsu.
“Yana da matukar dacewa gwamnati ta kara musu abin da suke samu a kowane wata, domin karfafa musu guiwa da tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali da inganci,” inji Ambassador Auwal Danlarabawa.
Gidauniyar Grassroot Care and Aid Foundation ta dade tana gudanar da ayyukan jin kai da tallafawa mabukata daga tushe, tare da kira ga hukumomi da al’umma gaba daya su goyi bayan duk wani mataki da zai inganta rayuwar masu hidima ga jama’a a kowanne lokaci.
Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF)