Featured
Rahotannin Da Ke Cewa Bello Turji Ya Miƙa Wuya Ga Sojoji Ba Gaskiya Bane – Hedikwatar Tsaron Najeriya

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa shugaban ’yan bindiga Bello Turji ya mika wuya ga sojoji.
Daraktan Hulɗar da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 14 ga Agusta, a birnin Abuja yayin wani taron bayani kan ayyukan rundunar.
“Da ya ke martani game da shugaban ’yan ta’adda, Bello Turji; Turji bai mika wuya ba, har yanzu muna ci gaba da neman sa,” in ji shi.
Turji, wanda ake nema ruwa a jallo, na gudanar da ayyukan ta’addanci musamman a jihohin Zamfara da Sakkwato, kuma ana zarginsa da shirya hare-hare da dama a kan al’ummomi a yankin Arewa maso Yamma.
Kwanan nan, an ruwaito cewa shugaban ’yan bindigar ya mika makamansa tare da sakin mutane 32 da aka yi garkuwa da su, a wani shirin sulhu da malaman addinin Musulunci a jihar Zamfara suka jagoranta.