Featured
Gwamnatin Kano Ta Amince Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Barau FC Ta Yi Amfani da Filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da Barau Football Club ta yi amfani da filin wasan Sani Abacha, Kofar Mata, a matsayin filin riko na gida a kakar 2025/2026 ta gasar Nigeria Premier Football League (NPFL).
Daraktan Yaɗa Labaran Kulob ɗin, Ahmad Hamisu Gwale, shi ne ya sanar da hakan a yau Talata 19 ga Agusta, 2025. Ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan wani taron sirri tsakanin jami’an Hukumar Wasanni ta Jihar Kano da kuma shugabancin Barau FC.
Asalin filin wasan Barau FC, Dambatta Stadium da ke Kano ta Arewa, na fuskantar gyare-gyare a halin yanzu, lamarin da ya sa aka nemi filin riko kafin sabuwar kakar ta fara.
Shugaban Barau FC, Ibrahim Shitu Chanji, ya bayyana a ranar Talata 19 ga Agusta, cewa Hukumar Wasanni ta jihar ta ba da amincewa ga kulob ɗin domin yin amfani da filin Sani Abacha har tsawon kakar.
“Da farko, muna godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabiru Yusuf, bisa wannan alfarma. Haka kuma Hukumar Wasanni ta saurari damuwarmu, ta kuma amince da buƙatarmu. Ba za mu manta da goyon bayan Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ba,” in ji Chanji.
Ya kara da cewa kulob ɗin na fatan samun cikakken goyon bayan jama’ar Kano, tare da yin kira ga masoya su nuna hali na kirki da zama jakadu nagari a duk lokacin da suke halartar wasannin kulob ɗin a wannan kakar.
Barau FC za ta fara karɓar bakuncin Enyimba FC a wasan buɗe kakan NPFL ranar Lahadi, 24 ga Agusta, 2025, a filin wasan Sani Abacha, Kofar Mata, Kano.