Featured
Jam’iyyar PDP Ta Yi Ƙarin Haske Kan Taron Da Ta Gudanar A Zamfara Duk Da Halin Rashin Tsaro Da Ya Addabi Jihar

Gwamnonin PDP sun yi ƙarin haske kan taron da suka gudanar a Gusau, Zamfara, a ranar Juma’a 22 ga Agusta da Asabar 23 ga Agusta, duk da hare-haren da suka faru a jihar. Jamiyyar ta soki ADC kan siyasantar da rayukan jama’a maimakon nuna tausayawa ga wadanda ibtila’i ya shafa.
Tun da farko kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara. Inda ya ce gwamnonin PDP sun nuna rashin tausayi ganin yadda su ka gudanar da taro a jihar, duk da cewa mutane da yawa sun rasa rayukansu kwanaki kaɗan da suka gabata.
Sai dai PDP ta mayar da martani ta bakin Darakta Janar na kungiyar gwamnonin Jam’iyyar PDP, Emmanuel Agbo, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin. Ya ce an dade da shirya taron, ba wani abu ne da aka ɗauka cikin gaggawa ba. PDP ta kara da cewa taron ya tattauna kan batun tsaro da sauran matsalolin ƙasa.
PDP ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Zamfara wajen kokarin daƙile matsalar tsaro, tare da alhinin kisan gilla a Katsina, Filato, Neja da Benue. Ta ce tun bayan barin wasu zuwa ADC, jam’iyyar ta ƙara ƙarfi.