Featured
NDLEA Ta Cafke Wani Mutum da kwalabe 8,000 na Akuskura A Kano
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta cafke wani mutum mai shekara 37 a Kano, dauke da kwalabe 8,000 na ruwan ganyen Akuskura da buhunan tabar wiwi guda 48. Kakakin hukumar reshen Kano, Sadiq Maigatari, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 02 ga Satumba, 2025.
An kama mutumin ne a yayin da jami’an hukumar suka dakatar da wani mai babbar mota a kan hanyar Zariya–Kano, kusa da Gadar Tamburawa. Motar dauke da kekunan NAPEP, inda aka samu kayan laifin a ɓoye tsakanin kekunan da kuma ƙasan tirelar, wanda aka yi katanga da katako domin rufe su. Jami’an NDLEA sun gano wannan dabara ne sakamakon tsananin kulawa da binciken da suka yi.
Dukkanin kayayyakin da aka kama tare da wanda ake zargi yanzu suna hannun hukumar NDLEA, inda ake ci gaba da bincike da kuma gwajin dakin gwaje-gwaje domin tabbatar da ainihin sinadaran. Kwamandan hukumar a Kano, ACGN AI Ahmad, ya godewa shugaban hukumar na ƙasa, Janar Mohammed Buba Marwa (rtd), bisa irin tallafi da goyon bayan da yake baiwa jihohi wajen gudanar da ayyuka cikin ƙwarewa.
A cikin watanni bakwai da suka gabata, NDLEA ta ƙara kaimi wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a fadin ƙasar, inda ta kama mutum 1,315 da ake zargi da safarar ƙwayoyi. Haka kuma ta kwace jimillar kilogram 1,387,254.27 na miyagun ƙwayoyi daban-daban, ciki har da tabar wiwi mai nauyin kilogram 126,168.73, da kuma lalata hekta 320 na gonakin wiwi guda 43 a jihohin Edo, Ondo, Cross River, Delta, Ekiti, da Osun.
