Featured
Idan Na Samu Cikakken Iko Kan Hukumomin Tsaro Zan Kawar Da Ta’addanci Cikin Watanni Biyu A Zamfara – Dauda Lawal

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa da zarar ya samu cikakken iko kan rundunonin tsaro a jihar, zai iya kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga cikin watanni biyu. Ya ce yana da sahihan bayanai da kuma wuraren da manyan shugabannin ’yan bindiga suke, amma matsalar ita ce dakarun tsaro a jihar ba sa karɓar umarni daga gare shi sai daga Abuja. Wannan, in ji shi, ya sanya sau da dama ba a ceto al’umma cikin gaggawa duk da cewa an san inda matsalar take.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta saka hannu sosai wajen tallafa wa rundunonin tsaro, duk da rashin ikon ba da umarni. Ya tuna cewa kimanin watanni biyu da suka gabata, gwamnati ta raba motoci masu sintiri 150 ga jami’an tsaro daban-daban tare da ɗaukar dubban matasa a matsayin Community Protection Guards (CPG), da kuma gayyato masu farauta daga jihohin Arewa maso Gabas domin taimakawa yaki da ’yan bindiga.
Ya kuma ce duk da rashin iko da yake da shi, yana ɗaukar nauyin kare rayukan al’ummar Zamfara a matsayin babban jami’in tsaro na jihar. Lawal ya bayyana cewa ko da matsalar ’yan bindiga tana da nasaba da rashin abinci, ruwa ko makarantu, shi a shirye yake ya samar da su don samun zaman lafiya a jihar.
Sai dai gwamnan ya koka da cewa akwai masu amfani da matsalar tsaro wajen siyasa don kawo cikas ga kokarin gwamnati. Ya yi kira ga jama’a da su yi haƙuri tare da nuna goyon baya, domin gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo ƙarshen wannan annoba ta ’yan bindiga.