Featured
A Takarda Kawai Tattalin Arzikin Najeriya Ya Ke Haɓɓaka Amma Ƴan Ƙasa Wahala Kawai Su Ke Sha – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu kan ikirarin da ya yi cewa tattalin arzikin Najeriya ya daidaita. Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi Oba Ghandi Afolabi Oladunni Olaoye, Soun na Ogbomosoland, inda ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun kawo ci gaba a Najeriya.
A jawabinsa, Tinubu ya yi ikirarin cewa an shawo kan matsalolin da suka daɗe suna hana ƙasar samun kuɗaɗen shiga, kamar smuggling, karya a lissafin tattalin arziki da rashawa. Ya ce matakan da suka ɗauka sun dakatar da ta’annati a harkar tattalin arzikin ƙasa, kuma yanzu an samu daidaito da kwarin gwiwa daga ƙasashen waje.
Sai dai a martaninsa, Obi ya ce idan wannan ikirari gaskiya ne, ya kamata a ga tasirin sa kai tsaye a rayuwar ‘yan Najeriya. Ya yi nuni da cewa kamata ya yi gwamnati ta daina ciyo bashi, ta biya manyan basussuka da ake bin gwamnati, sannan ta saka hannun jari a ayyukan da suka daɗe ba su samun isasshen kuɗi ba.
Obi ya ƙara da cewa sahihin cigaba ba a cikin alkaluma kawai yake ba, sai a makarantu da asibitoci da sauran muhimman wuraren rayuwa. Ya bukaci gwamnatin Tinubu ta mayar da kuɗaɗen da ake samu zuwa bangaren lafiya, ilimi da fitar da jama’a daga talauci cikin gaskiya da tsantseni, domin a tabbatar cewa ci gaban tattalin arzikin da ake faɗi ya shafi kPeter Obi owa.