Connect with us

Featured

Gwamnatina Ta Dawo Da Darajar Najeriya A Idon Duniya – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa manyan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekaru biyu sun farfado da martabar Najeriya a duniya tare da daidaita tattalin arzikin kasar. Ya ce daukar matakan kawar da rashawa, da cin hanci a harkokin kudade da man fetur ya hana kasa ci gaba, amma yanzu mun yi maganin abun, kasar ta dawo hayyacinta.

Shugaban ya kara da cewa kafa NELFUND ya tabbatar da cewa babu dalibi da zai daina karatu saboda talauci, domin ilimi shi ne mafi girman makami da za a iya bai wa dan Adam don ya fita daga talauci. Haka kuma ya ce gwamnati na ci gaba da zuba jari a fannin ababen more rayuwa, duk da cewa shekaru biyu kacal aka yi da hawa mulki.

A nasa jawabin, Soun na Ogbomosoland, Oba Ghandi Olaoye, ya yaba wa Tinubu bisa jarumtar cire tallafin man fetur da gyaran harkar kudade, da ya ce sun tabbatar da sahihancin jagoranci. Ya kuma gode wa Shugaban kasa saboda kwangilar hanyar Oyo-Ogbomoso da aka sake farfado da ita, wacce ya ce za ta inganta kasuwanci da hada kan Arewa da Kudu.

Sai dai Sarkin ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi duba kan batun samar da ruwa da wutar lantarki a Ogbomoso, da sabunta Asibitin Gwamnati zuwa matsayin Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, da kafa cibiyar bincike kan amfanin ayaba da kaji na Ogbomoso. Haka kuma ya gode wa Tinubu bisa nada mutanen garin cikin gwamnati, ciki har da Shugaban FIRS, Zacch Adedeji.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet