Featured
Ɗaurarrun Da Su Ka Shafe Shekara 6 A Gidan Gyaran Hali Ba Tare Da An Gurfanar Da Su A Gaban Kotu Ba Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

Babbar Alkaliyar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu-Aboki, ta umarci sakin fursunoni shida da suka shafe dogon lokaci a kurkuku ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba. Wannan mataki ya zo ne yayin da ake fama da matsalolin jinkirin shari’a da cunkoson gidajen gyaran hali a Najeriya.
A cewar sanarwar Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Kano, waɗanda aka saki sun kasance cikin irin waɗanda aka kasa gudanar da shari’a saboda ɓacewar fayil ɗin shari’a, rashin ci gaba daga masu gurfanarwa, da jinkirin tsarin kotuna. Mai Shari’a Abdu-Aboki ta bayyana cewa matakin na daga cikin kokarinta na gyara tsarin shari’a da kuma rage tsawon lokacin da ake tsarewa mutane kafin shari’a.
Ta bukaci haɗin kai daga ƴan sanda, ofishin Babban Lauyan Kano, da Hukumar Gyaran Hali domin tabbatar da shari’a cikin lokaci da rage tsare-tsare ba tare da gurfanarwa ba. Haka kuma ta ja hankalin waɗanda aka saki da su guji laifi su zama nagartattun ƴan ƙasa.
Shugaban Hukumar Gyaran Hali na Kano, Ado Inuwa, ya yi kira ga fursunonin da aka saki da su kiyaye doka, tare da yabawa shugabancin hukumar ta kasa bisa samar da shirye-shiryen koyar da sana’o’i da ilimi domin taimaka musu wajen zama masu dogaro da kai bayan an sake su.