Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Za Ta Ci Tarar 500,000 Ga Masu Sare Bishiya Ba Tare Da Izini Ba

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta amfani da Injin Sare Bishiya ba tare da lasisi ba, wajen sare ko gyaran bishiyoyi, domin yakar sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba da kuma kare muhalli. Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad-Hashim, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Kano, inda ya ce matakin ya samu goyon baya daga kundin tsarin mulki na 1999 da dokokin muhalli na kasa.

An ƙirƙiri tsarin lasisi na musamman mai suna Chainsaw Usage Permit Framework (CUPF) wanda ya ƙunshi rukuni biyu: CUPF-A don masu sana’ar sare bishiyoyi da ’yan kasuwa, da kuma CUPF-B wanda ya zama wajibi ga duk wanda zai sare ko yanke bishiya a wuraren jama’a. Kowace bishiyar da aka sare dole a maye gurbinta da sabbin dashe guda biyu ko uku.

Domin tabbatar da bin doka, an samar da rajistar lasisi ta zamani da QR code, sannan za a yi aikin sa ido tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, kananan hukumomi. Hukuncin masu karya doka ya hada da tara naira dubu 500,000, ko yiwuwar zaman gidan yari. Haka kuma, duk wanda ya sare bishiya ba tare da lasisi ba zai biya tara naira dubu 250,000 kowace bishiya tare da sake dasa sabbi.

Kwamishinan ya bukaci shugabannin kananan hukumomi, makarantun Islamiyya, masallatai, malamai, da sarakunan gargajiya su taimaka wajen wayar da kan jama’a game da illar sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba. Ya jaddada cewa gwamnatin Kano na da cikakken kudiri na kare dazukan jihar.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet